Zakaran Formula 1 na duniya Rosberg ya yi ritaya

Nico Rosberg

Asalin hoton, AFP

Zakaran tseren motocin Formula 1 na duniya Nico Rosberg ya sanar da cewa ya yi ritaya nan take.

Dan tseren dan kasar Jamus mai shekara 31 ya ci babbar gasarsa ta farko ranar Lahadi, bayan ya doke Lewis Hamilton.

Rosberg ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa "Na kai kololuwar ganiyata don haka wannan matakin da na dauka shi ne ya dace."

Rosberg ya lashe manyan gasar tseren motoci tara cikin 21 da aka yi a bana, inda ya doke Hamilton wanda sau uku yana zama zakaran tseren.

Ya kara da cewa,"A shekara 25 da na yi ina yin tseren motoci, babban burina shi ne na zama zakaran Formula 1 na duniya."