China ta gargadi Donald Trump kan Taiwan

Donald Trump ya ce ya taya shugabar Taiwan murnar lashe zaben watan Janairu

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Donald Trump ya ce ya taya shugabar Taiwan murnar lashe zaben watan Janairu

Ma'aikatar harkokin wajen China ta ce ta shigar da korafi kan wayar tarhon da shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya yi da shugabar kasar Taiwan.

China na kallon Taiwan a wani bangare nata da ya balle.

Dokokin Amurka sun sa kasar ta katse duk wata hulda da Taiwan a hukumance tun a shekarar 1979.

Amma kwamitin karbar mulki na Mr Trump ya ce Trump din da Shugaba Tsai Ing-wen sun bukaci yin "hulda ta kut-da-kut da juna kan kasuwanci da siyasa da kuma tsaro", lokacin wayar da suka yi.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

China na sanya ido sosai kan Trump

China ta ce ta mika "koke na musamman" ga gwamnatin Amurka.

Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya ambato mahukuntan kasar China na bukatar Amurka da "ta yi takatsantsan kan huldarta da Taiwan domin gujewa abin da zai shafi dangantaka tsakanin China da Amurka".

Tun da farko dai wasu rahotanni sun ce ministan harkokin wajen China Wang Yi ya bayyana wayar da shugabannin biyu suka yi a matsayin wata "babbar yaudara daga bangaren Taiwan."

Trump ya taya Taiwan murna

Mr Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa Ms Tsai ce ta kira wo shi domin ta yi masa murnar lashe zaben Amurka.

Masu magana da yawunsa sun ce shi ma ya taya ta murnar zama shugabar Taiwan a zaben da aka yi a watan Janairu.

Wayar da Mr Trump ya yi kai-tsaye da shugabar Taiwan abu ne da ba a saba ganin wani shugaban Amurka ya yi ba.

China tana da daruruwan makamai masu linzami jibge suna kallon Taiwan, kuma ta yi mata barazanar yin amfani da karfin soja idan ta nemi zama mai cin gashin kanta.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Ms Tsai ce mace ta farko da ta zama shugabar Taiwan