Matar da ta ajiye digirinta domin sayar da koko

Bayanan sauti

Dalilin da ya sa na ajiye digirina domin sayar da koko

A ci gaba da shirin BBC na mata 100 muryar rabin al'ummar duniya, mun yi hira da Zakiyya Sulaiman wata matashiya a Ghana wacce ta kammala karatunta na jami'a a shekarar 2013 kuma ta ajiye kwalinta tana sayar da koko.

Tun kafin zakiyya ta kammala hidimar kasa ta fara neman aiki, amma shekara biyu bayan nan ba labari.

Zakiyya ta yi tunani a kan irin kasuwanci da ta ga ya dace ta fara domin ta magance wani kalubale da al'mma ke fuskanta mussaman a fannin abinci.

Ta ce a Ghana koko na daya daga cikin abincin da al'ummar hausawa da ma wasu mutane da dama suke matukar so.

Amma a lokuta da dama aiki ba ya bai wa mutane damar iya hada koko da kansu a gida saboda gudun kar su bata lokaci wajen hadawa.

Zakiyya ta bayyana cewa wannan shine dalilin da yasa ta fara tunanin lokaci ya yi da ya kamata a ce ta fara neman na kanta ba kawai don taimakawa iyayenta ba, har ta samar da wata maslaha ga al'umma.

Ku saurari hirar da wakilinmu Ibrahim Isa ya yi da Zakiyya inda ta fara bayyana yadda ta kirkiri wani kamfani mai sarrafa garin koko mai suna Zacky foods.