Dalilin da ya sa na ajiye digirina domin sayar da koko

A ci gaba da shirin BBC na mata 100 muryar rabin al'ummar duniya, mun yi hira da Zakiyya Sulaiman wata matashiya a Ghana wacce ta kammala karatunta na jami'a a shekarar 2013 kuma ta ajiye kwalinta na digiri tana sayar da koko.