Rayuwar 'yan gudun hijira a hotuna

A fallon a baje kolin hotuna sama da 30 na 'yan gudun
Ga mutane da dama a Abuja, babban birinin Najeriya, hotunan 'yan gudun hijira da aka baje dama ce ta gane wa idanuwansu wadansu daga cikin abubuwan da suke dade suna jin labarinsu.
Dubban daruruwan mutane ne dai rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu, musamman a arewacin Najeriya, baya ga fiye da 2,000 da suka riga mu gidan gaskiya.
Ko da yake masu ruwa-da-tsaki sun ce fiye da kashi sittin cikin dari na mutanen da suka tsere daga gidajensu na zaune ne tare da 'yan uwa da abokan arziki a wadansu garuruwan, wadanda rikicin ya shafa da dama na neman mafaka ne a sansanonin 'yan gudun hijira a sassa daban-daban na kasar.
Galibin 'yan gudun hijirar dake wadannan sansanoni dai na cikin wani mawuyancin hali, amma imanin wasunsu kan taka muhimmiyar rawa wajen sama musu nutsuwa.
Wannan mayar da hankali ga addini daya ne daga cikin jigon hotunan da wasu masu sana'ar daukar hoto suka baje kolinsu, inda suka bayyana yadda 'yan gudun hijira masu yawa ke mayar da al'amuransu ga ubangijinsu.
Domilita ta ce makasudin yin baje kolin hotunan shine ta isar da sako ga masu kallonsu
Hotunan da Domitila Modesty ta dauka ne suka fada a karkashin wannan jigo na rawar da addini ke takawa a rayuwar 'yan gudun hijirar da ke sansanoni.
Domilita 'yar kasar Argentina ce haifaffiyar birnin Kaduna da ke arewacin Najeriya.
Ta ce, "Ina yawan tunanin Najeriya, musamman bayan da rikicin Boko Haram ya barke".
'Yan gudun hijirar da dama sun dogara ne kacokan kan addininsu wanda suka yi amannar shi hanyar da zasu samu kwanciyar hankali
Asalin hoton, BBC Sport
A mafi yawan lokuta sun taruwa ne a wuraren da suke ibada domin su yi addu'a
Domitila, wadda ke yi wa kanta lakabi da Sa'adatu, ta kara da cewa, "A matsayina na mace, mai tausayi, na yi amfani da damar baje kolin ne domin na isar da sako game da halin matsin da 'yan gudun hijira ke ciki ga 'yan Najeriya".
Ire-iren hotunan Domitila na nuni da cewa 'yan gudun hijira da dama sun karkata ga addininsu wanda a ganinsu shi kadai ne hanyar da za su bi domin samun sanyi a zukatansu.
'Yan gudun hijira da ke sansanonin daban-daban na sassan Najeriya na da burace-burace da su ke so su cimma
Ramin Hashempour ma ya yi amfani da hotuna wajen bayyana wa mutane irin halin kuncin da 'yan gudun hijrar ke ciki.
"Kyakkyawan Fata" shi ne jigon hotunan da Mista Hashempour ya baje kolinsu. A cewarsa, "Duka hotunan suna da sakonnin da suke so su isar ga masu kallonsu na irin rayuwar da 'yan gudun hijira ke yi a sansanonin 'yan gudun hijira dake sassa daban-daban na kasar nan".
Fatan 'yan gudun hijira da dama shi ne su zama masu dogara da kansu
Wannan buri na Domitila da Ramin (na isar da sako game da halin 'yan gudun hijira) ya sa kungiyoyi da dama kamar su FashionForCharity da gidauniyar TY Danjuma suka hada gwiwa da su don koya wa wasu 'yan gudun hijirar sana'oi daban-daban domin su dogara da kansu su kuma iya daukar nauyin bukatunsu na yau da kullum.