'Zai wuya El-Zakzaky ya zauna a wani gari ba Zaria ba'

Ta kuma ce a biya shi diyya tare da matarsa ta Naira miliyan 50
Bayanan hoto,

Kotu a Najeriya ta ba da umarnin sakin Elzakzaky

Kungiyar 'yan uwa Musulmai ko kuma Islamic Movement of Nigeria bai bin tafarkin Shi'a, ta ce, ta yi farin ciki da hukuncin da babbar kotun Abuja ta yanke na a saki shugabanta, Sheikh Ibrahim Zakzaky.

A ranar Juma'a ne dai alkalin wata babbar kotun Najeriya, Mai shari'a Gabriel Kolawole, ya yanke cewa gwamnati ta saki Elzakzaky cikin kwana 45.

Sannan kuma a ba shi diyya shi da mai dakinsa ta Naira Miliyan 25 kowanennen su.

Kotun ta kuma umarci gwamnati da ta gina wa shugaban na IMN gida a duk inda yake so kasancewar an ruguje gidansa.

To sai dai wasu jiga-jigan 'ya'yan kungiyar sun fara yin tsokaci dangane da batun sake gina gidan a Zaria ko kuma a wani gari daban.

Malam Abdulhameed Bello wanda shi ne jagoran 'yanuwa musulmin a Zaria, ya ce, sun yi murna da jin hakan amma fa ba ya tunanin El-zakzaky zai so zama a wani gari sabanin mahaifarsa, Zaria.

Tun dai watan Disamba Elzakzaky yake tsare a hannun gwamnatin Najeriya, bayan wani farmaki da sojojin kasar suka kai wa mabiyansa bisa zargin yunkurin halaka babban hafsan sojin kasar.