Zan bi ƙa'ida wajen gurfanar da Jammeh — Barrow

Barrow

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Adama Barrow, wanda mai hada-hadar gidaje ne, na da farin-jini a wurin matasa

Shugaban kasar Gambia mai jiran gado, Adama Barrow, ya ce, idan har akwai yiwuwar gurfanar da shugaban kasar mai barin gado, Yahya Jammeh, to za a bi ka'ida wajen hakan.

Adama Barrow ne dai ya kayar da Yahya Jammeh da tazarar kuri'a fiye da 50,000.

Mutane suna ta yin kira da a gurfanar da Yahya Jammeh bisa ayyukan take hakkin jama'a da ake zargin ya aikata.

To amma Mista Barrow ya shaida wa BBC cewa watakila za a iya yin hakan amma fa bisa ka'ida.

Ya ce bai kullaci kowa a ransa ba ballantana ya yi masa bita-da-kulli irin ta siyasa.

Shugaban kasar mai barin gado Yahya Jammeh ya amince da shan kaye bayan da ya kira Adama Barrow ta waya, a inda ya taya shi murnar cin zaben.