An kai gawarwakin 'yan kwallon Brazil gida

'Yan jarida 20 sun mutu a hatsarin

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

'Yan jarida 20 sun mutu a hatsarin

An kai gawarwakin 'yan kwallon Brazil din nan 71 da suka mutu a Colombia sakamakon hatsarin da jirginsu ya yi kasar a yayin da ake shirin yi musu jana'iza.

Ana sa ran fiye da mutum 100,000 za su halarci jana'izar tasu a filin wasan da ke Chapeco a ranar Asabar.

Mutum shida ne kawai suka rayu bayan hatsarin da jirgin ya yi ranar Litinin a kusa da Medellin, inda suka je domin yin wasan da 'yan kasar Columbia.

Shugaban Brazil Michel Temer na shirin yin maraba da gawar tasu a filin jirgin saman kasar.

Sai dai ba a sa ran zai halarci jana'izar saboda rahotannin da ke cewa za a yi zanga-zanga a wajen.

Amma shugaban hukumar kwallon kafar duniya, Fifa, Gianni Infantino zai halarci jana'izar.

Daruruwan mutane ne suka taru a kan titin filin jirgin saman Medellin ranar Juma'a domin nuna girmamawa ga gawarwakin 'yan wasa.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

'Yan kasar Bolivia na cikin wadanda hatsarin ya rutsa da su

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An mika gawar ma'aikacin jirgin dan kasar Paraguay ga mahaifinsa

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Magoya bayan 'yan wasan sun yi makoki a filin wasan Arena Conda