'Dakarun tsaro sun kwace kashi 60 na Aleppo daga hannun IS'

Syrian pro-government forces set up an outpost on December 2, 2016 in the Aleppo"s eastern neighbourhood of Sakan al-Shababi

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Jami'an tsaron Syria sun kwace kusan kashi biyu cikin uku na yankunan gabashin birnin Aleppo da ke hannun mayakan kungiyar IS.

Wata kungiyar da ke sanya idanu a kan fafatawar da ake yi a Syria wacce ke da mazauni a Birtaniya ta ce sojoji sun kwace lardin Tariq al-Bab ranar Juma'a, inda aka samu hanya daga yankin da ke hannun gwamnati zuwa filin jirgin saman Aleppo.

Sojojin sun kwace yankuna da dama na gabashin birnin daga wajen IS a mako ukun da suka wuce.

Har yanzu akwai kimanin mutum 250,000 da fadan ya rutsa da su a cikin birnin.

Dubban mutane ne suka rasa muhallansu sakamakon gwabzawar da ake yi tsakanin dakarun gwamnati da mayakan na IS.

Majalisar dinkin duniya ta ce gabashin birnin na Aleppo na cikin mummunan hali har ta kai ana yi wa mutane tiyata ba tare da an yi musu allurar kashe zafi ba.

An kashe akalla mutum 300 a gabashin birnin sun lokacin da dakarun gwamnati suka kaddamar da hare-haren fatattakar mayakan IS din.