Apple zai fara kera mota mara matuki

Apple logo

Asalin hoton, Getty Images

Kamfanin Apple ya ce yana shirin soma kera motoci marasa matuka.

A wata wasika da ya aike wa hukumar da ke sanya ido kan sufuri ta Amurka, Apple ya ce yana "matuka murna kan yadda fannin fasaha ke sauyawa ciki har da fannin sufuri".

Ya kara da cewa al'uma za ta mori sauye-sauyen da ake samu a motocin da ake kerawa marasa matuka.

An dade ana rade-radin cewa Apple zai soma kera motoci marasa matuka, amma sai yanzu kamfanin ya tabbatar da batun.