An bukaci a binciki Mourinho kan zille wa biyan haraji

Jose Mourinho

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ana zargin Jose Mourinho da yin amfani da kamfanonin kasashen waje domin kauce wa biyan haraji

Wata 'yar majalisar dokokin Birtaniya ta bukaci a yi cikakken bincike kan Jose Mourinho bayan wasu rahotanni sun nuna cewa ya kauce wa biyan haraji.

Ana zargin Mourinho da kai miliyoyin fan tsibirin Virgin Islands da zummar zille wa biyan haraji.

Sai dai wakilin kocin na Manchester United ya ce babu kanshin gaskiya a wannan zargi.

'Yar majalisa Meg Hillier, wacce ke shugabancin kwamitin sanya ido kan yadda hukumomi ke kashe kudi, ta shaida wa jaridar Sunday Times cewa ya kamata "a yi kwakwaran bincike" kan wannan batu.

Jaridu da dama a kasashen Turai sun wallafa zargin cewa Mourinho - da wasu manyan 'yan wasan duniya - sun zille wa biyan haraji.

Wasu bayanai da aka kwarmata ne suka nuna cewa mutanen, cikin su har dan wasan Real Madrid Christiano Ronaldo, sun kauce wa biyan haraji.

Wasu rahotanni sun ce Mourinho, mai shekara 53, ya yi amfani da wani kamfanin Virgin Islands domin sanya £10m a wani asusu a wani bankin Switzerland.

Sunday Times ta ce shi ma Ronaldo ya yi amfani da asussa da kamfanoni daban-daban a kasashen Ireland, Switzerland da kuma New Zealand domin samun kudi ta hanyar amfani da matsayinsa.

Sai dai Jorge Mendes, wakilin Mourinho da Ronaldo, ya musanta zargin.

Ya kara da cewa dukkan mutanen suna bin dokokin Birtaniya da Spain na biyan haraji.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Ana zargin Cristiano Ronaldo da zille wa biyan haraji

Amma 'yar majalisar dokokin ta shaida wa BBC cewa: "Ina gani yana da matukar muhimmanci hukumomin da ke karbar haraji su yi cikakken bincike kan wannan batu kuma mu ma za mu taso da wannan batu ranar Laraba a zauren majalisa."

Ta kara da cewa zargin zai kashe gwiwar 'yan kallo wadanda ke kashe kudadensu wajen sayen tikitin wasa.

Kungiyar Real Madrid ba ta ce komai a kan zargin da ake yi wa dan wasanta ba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jose Mourinho and Cristiano Ronaldo lokacin suna tare a Real Madrid