Yarinyar da ke ba duniya labarin yakin Aleppo ta 'bata'

Sakonnin Twitter da Bana Alabed ke aika wa sun ja hankalin duniya

Asalin hoton, @alebedbana

Bayanan hoto,

Sakonnin Twitter da Bana Alabed ke aika wa sun ja hankalin duniya

An daina jin duriyar yarinyar nan 'yar shekara bakwai wacce ke aike wa da sakonni Twitter daga Aleppo na Syria kan fafatawar da ake yi a birnin a daidai lokacin da aka kaddamar da sabon yunkurin sake kwace birnin daga hannun 'yan kungiyar IS.

Bana Alabed tana aike wa da sakonnin ne da harshen Turanci tare da taimakon mahaifiyarta, wacce malamar makaranta ce.

Amma an kulle shafin nata ranar Lahadi, a yayin da dakarun sojin kasar ke kutsa wa yankin gabashin birnin da ke hannun 'yan tawaye.

Sakon karshe da mahaifiyarta ta wallafa a shafinta na cewa: "Muna da tabbacin cewa sojoji za su kama mu yanzu haka. Za mu gana wataran da ku al'umar duniya. Sai wataran. - Fatemah".

Aleppo, birni na biyu mafi girma a Syria, ya rabu zuwa bangare biyu tun lokacin da aka fara yaki. Bana na zaune ne a gabashin birnin da ke hannun 'yan tawaye, inda dakarun sojin kasar ke yi wa luguden wuta.

Sojojin sun shiga yankin a daren Lahadi bayan sun gama barin-wuta.

Asalin hoton, @alabedbana

Bayanan hoto,

Bana da 'yan uwanta maza biyu

Shafin Bana na Twitter ashi ne - @alabedbana - kuma tana da mabiya sama da 100,000.

Ta ja hankalin duniya ne sakamakon sakonnin da ita da mahaifiyarta ke aika wa kan halin da farar-hula ke ciki a Aleppo.

A watan Oktoba, mahaifiyar Bana ta shaida wa BBC cewa 'yarta tana son "duniya ta ji halin da muke ciki".

Asalin hoton, @alabedbana

Asalin hoton, @alabedbana

An kashe akalla mutum 300 tun lokacin da dakarun gwamnati suka kaddamar da hare-hare domin sake kwace gabashin Aleppo kuma rahotanni na cewa an rutsa da kusan mutum 250,000.