Kamfanonin sadarwa na yaki da ta'addanci

Rumbun zai gano hotuna da bidiyon da ke watsa ta'addanci

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rumbun zai gano hotuna da bidiyon da ke watsa ta'addanci

Kamfanonin Facebook, Microsoft, Twitter da kuma YouTube na hada gwiwa domin hana duk wani nau'i na tayar da hankali da tsattsauran ra'ayin addini da ake wallafa wa ta hanyar hotuna ko bidiyo a dandalinsu.

Kamfanonin guda hudu sun sha alwashin kirkiro wata manhajar ajiye bayanai na intanet da za ta rika gano duk hoto ko bidiyon da za a sanya da nufin ta'addanci ko tayar da zaune-tsaye.

Da zarar manhajar ta gano hakan, za a sanar da dukkan kamfanonin ta yadda za su dauki matakin hana wallafa shi a shafukansu.

Wata sanarwa da kakakin Twitter ya sanya wa hannu ta ce, "Ba za mu bari a rika amfani da kamfanoninmu wajen watsa ta'addanci ba."

Ya kara cewa babban fatansu shi ne a rage yawan ta'addancin da ake watsawa ta hanyar intanet.

Kamfanonin hudu sun dauki wannan mataki ne a daidai lokacin da hukumar tarayyar Turai ta yi kira a gare su da su hanzarta daukar matakin hana yin kalaman kiyayya a shafukan nasu.