Cazeneuve ya zama sabon Firai Ministan Faransa

Bernard Cazeneuve

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mr Cazeneuve ya yi suna bayan da ya sha alwashin murkushe mayakan IS

An nada ministan cikin gida na Faransa Bernard Cazeneuve a matsayin sabon Fira Ministan kasar, domin maye gurbin Manuel Valls, wanda ya yi murabus domin tsayawa takarar shugaban kasa a shekara mai zuwa.

Mr Valls ya mika takardar murabu dinsa ga shugaban kasar Francois Hollande ranar Talata.

Mr Cazeneuve zai zama shugaban gwamnatin gurguzu har zuwa watan Yuni lokacin da za a yi zaben majalisar dokoki.

Ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaron kasar tun lokacin da mutanen da ake zargi 'yan ta'adda ne suka kai hari a birnin Paris shekarar da wuce.

A watan gobe ne Mr Valls zai fafata da sauran masu son yi wa jam'iyyar ta 'yan gurguzu takara a zaben fitar da gwani.