An kama mutanen da suka bude ofishin jakadancin Amurka na bogi a Ghana

Asalin hoton, State Department
Mutane da dama da suka samu bizarsu ta wannan hanyar sun tafi Amurka
Jami'an tsaron kasar Ghana sun kama akalla mutum uku da ake zargi da hannu a kafa ofishin jakadancin Amurka na bogi a kasar.
Mutanen dai sun shafe shekara 10 suna tafiyar da ofishin jakadancin da ke babban birnin Ghana, Accra.
'Yan damfaran -- wadanda har yanzu ba a tabbatar da adaddinsu ba -- asirinsu ya tonu ne sakamakon wani bincike na hadin gwiwa da aka yi tsakanin ma'aikatan ofishin jakadancin Amurka da 'yan sanda.
Rahotanni na cewa mutanen na bai wa 'yan sandan hadin kai.
'Yan damfarar dai na samun kwastomomi ne daga Ghana da kasashen makwabtaka da ke yammacin Afirka su kai su cikin wani gini a Accra inda aka kafa tutar Amurka.
Suna karbar $6000 a wajen masu neman bizar Amurka sahihiya, lamarin da ake gani watakila ma'aikatan ofishin jakadancin na da hannu a badakalar.
Mutanen 'yan kasar Ghana ne da Turkiya.
An kwashe shekaru da dama ana wannan damfarar saboda masu neman bizar ba su taba zuwa ofishin jakadancin Amurka na gaskiya ba.
Akasarin masu zuwa ofishin jakadancin na bogi 'yan kauye ne.