CAR: An samu sojoji 41 da laifin aikata lalata

Dakarun da aka bincike su sun fito ne daga kasashen Burundi da Gabon

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Dakarun da aka bincike su sun fito ne daga kasashen Burundi da Gabon

Wani mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya, Stephane Dujjaric, ya ce wani bincike da aka gudanar da zarge-zargen cewa dakarun kiyaye zaman lafiya a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, sun aikata lalata ta fuskar jima'i, ya gano mutane arba'in da daya da suka aikata laifin.

Ya ce ashirin da biyar daga cikinsu daga Burundi suke, goma sha shida kuma daga Gabon.

Majalisar ta dinkin duniya ta ce alhakin gudanar da karin bincike kuma ya rataya a wuyan kasashen na Burundi da Gabon, domin a karkashin dokokin ayyukan kiyaye zaman lafiya, kasashe da suka samar da dakaru na da hurumin gurfanar da dakarunsu da suka aikata laifuka.

Su ma dai ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na Faransa da Majalisar Dinkin Duniya, an zarge su da aikata laifuka daban-daban da suka shafi lalata a kasar ta Jamhuriyar Tsakiyar Afirka.