Mata 100: ko kun san Iyayen da ke da-na-sanin haihuwa?

Hoton yaro da mahaifiyarsa

Asalin hoton, iStock

Shahararriyar marubuciyar kasar Faransa Corinne Maier na da yara guda biyu amma kuma ta kagu karamin cikinsu ya bar gida, tana mai cewa sun "gajiyar da ita kuma sun sa ta talauce".

Sukar da ta yi a kan "muhimmanci da ake bai wa zama iyaye" ya jawo hankulan iyaye a sassan duniya daban-daban.

Ga wasu daga cikin ra'ayoyinsu da kuma ra'ayoyin wadanda basu goyi bayan ra'ayinta ba.

Da-na-sani

A ra'ayin Alex, da ke birnin San Antonio, cewa ta yi na ji dadi kwarai da ya kasance cewa ba ni kadai ba ce uwar da ke jin cewa na rasa wasu abubuwa a rayuwata kasancewata uwa. A yayin da nake matukar son yara na, a yanzu sai nake ji cewa da na sani da ban haife su ba.

Ba wai kawai kashe kudi mutum yake yi wajen ba su kulawa ba, amma kuma basu tarbiyya ma na shafar abubuwa kamar samun cigaba a wajen aiki..

Ban taba kasancewa a matsayin wacce ke da kyakkyawar alaka da yara ba kuma har yanzu ma hakan ne.

Shekarar yaro na shida kuma har yanzu ba na iya wata hulda da shi da abokansa. A lokuta dama ba na so na kasance a matsayin uwa kuma ban dace da wannan matsayin ba. Ina ji na kamar wata bare a cikin iyaye mata wadanda ke da kyakkyawar alaka da yaransu.

Sai kuma ra'ayin Mary Edinburgh da ke cewa abu ne mai wahala in ce na yi da-na-sanin haifar yara na saboda ina matukar sonsu.

Amma da zan iya mayar da hannun agogo baya, bana jin zan damu da haihuwa. Kasancewa uwa na da dadi ne kawai a wasu lokutan.

Da basa nan zan yi kudi kuma na samu 'yanci na, kuma ba zan zamo ina da damuwa da yawa ba.

Asalin hoton, iStock

Bayanan hoto,

Bai wa yara tarbiyya na bukatar lokaci sosai idan dai har ana so su samu kyakkyawar tarbiyya

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Shekarata 50 kuma yanzu tattalin arzikina ya durkushe. Tabbas zama uwa ba na kowace mace ba ce saboda kasancewar muna da damar iya haihuwa ba yana nufin mu ke da wuka da nama ba.

Na yi duk abin da zan iya amma kuma na samu jin dadi? A'a. Da a ce zan sake rayuwata tun daga farko da ba zan taba haihuwa ba, in ji Joy Bath.

Jennifer daga Hertfordshire ta ce rainon yara ya gajiyar da ni da miji na kuma ba a nan kawai ya tsaya ba, akwai batun kula da su har su kai shekara 24 da 26.

Mun yi kokari sosai saboda mu ga cewa sun kasance masu dogaro da kansu amma mun kasa. Ba tare muke da su ba amma kullum muna yi musu hidima.

Ina son su duka, amma da a ce za a sake bani zabi da ba zan haihu ba.

Tsaka-Tsaki

Ina sha'awar gani na a matsayin uwa ko uba. Amma kuma ba abu ne da nake yi wa yarana fata ba.

Rayuwa tana sauyawa kuma ana cigaba da samun sauyi ta yadda mutum zai iya rayuwa ta jin dadi ba tare da ya yi aure ya tara iyali ba.

Za ka iya kasencewa cikin rayuwar jin dadi ba tare da rainon wasu ba. Idan kana da aikin yi mai kyau zai iya debe maka kewa a wasu karnin masu zuwa a cewar Jean daga garin Troon.

Sako daga Anja daga garin Maastricht na cewa ina da yara maza biyu kuma ina matukar sonsu kuma ba na taba gajiya har sai lokacin gajiyar ya kai kuma hayaniyarsu kullum karuwa take yi.

Asalin hoton, iStock

Bayanan hoto,

Iyaye mata da dama na cewa haihuwa na hana su samun cigaba a wuraren aikinsu

Da farko ina hakuri sosai kuma kwakwalwata na iya dauka. Amma yanzu duk na nemi wadannan abubuwa na rasa.

Rainonsu ya hada da tsara lokutan bacci da na cin abinci da saka tufafi da gyara wuri da basu tarbiya ta gari da kuma irin abubuwan da ya dace ka fada da kuma wanda bai dace ba, kuma a bangare daya kana kokarin tausar zuciyarka.

Ba na da-na-sani

Haihuwa ce abu mafi kyau da na taba fuskanta a rayuwata. Aiki ne kuma babba.

Ban san inda wani zai yi zaton cewar zama uwa ko uba abu ne mai sauki ba wanda zai haifar da jin dadi nan da nan.

A ko wanne irin yanayi, jin dadi abu ne da mutum zai nemawa kansa, in ji Brain daga jihar Ohio da ke Amurka.

Sai Karen da ke jihar Virginia, wacce ta ce ban taba tunanin ba zan haihu ba. Ina iya tuna lokacin da na shaida wa mahaifiyata cewa muna jira har sai lokacin da muka yi kudi kafin mu haihu.

Asalin hoton, iStock

Bayanan hoto,

Wasu iyayen suna cewa idan da ba a haihuwa a duniya da ba su samu cigaba a rayuwa ba

Sai ta ce, "idan jira kuke yi har sai kunyi kudi kafin ku haihu, ba za ku taba haihuwa ba". Muna da yara da jikoki saboda sun kara wayar mana da kawunanmu a kan abubuwan rayuwa kuma akwai yadda suke kallon abubuwa daban da ke faranta mana.

Ina alfahari kasancewa ta uwa - Haihuwa da kuma kula da abin da ka haifa abin farin ciki ne kuma yanzu yara na suna jami'a kuma suna dogaro da kansu.

Na kagu su haifi nasu yaran ta yadda zan iya kula musu da su.

Bai wa yara tarbiyyar da ta dace abu ne da ke saka mutum farin ciki. Za su taso suna masu godiya da irin tarbiyyar da ka basu, in ji Ghada da dake unguwar Enfield a Ingila.