Dominic Ongwen ya shaida wa ICC ba shi da laifin yaki

Asalin hoton, Reuters
Ana zargin Mr Ongwen da kai hari a sansanin 'yan gudun hijira
Kwamandan kungiyar 'yan tawayen LRA da ke Uganda, Dominic Ongwen, ya shaida wa kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke Hague, ICC bai aikata laifukan yaki ba.
Mr Ongwen ya kara da cewa kungiyar ta LRA ce ke da alhakin aikata laifukan, yana mai cewa ita ce ta sace shi sannan ta sa shi ya zama dan tawaye.
Kungiyar ce ta sace Ongwen, wanda yanzu yake da kusan shekara 40, lokacin yana yaro.
Ana zargin sa da aikata laifukan yaki da na cin zarafin bil adama a Uganda guda 70.
Ana zargin Mr Ongwen da jagorantar 'yan tawaye domin kai hare-hare a sansanonin 'yan gudun hijira guda hudu da ke arewacin Uganda, inda suka kashe tare da gallawa jama'a, kana suka tilasta wa mata aurensu da kuma sanya yara suka zama mayakan kungiyar.
Sai dai ya shaida wa kotun ICC cewa ya kamata a tuhumi kungiyar LRA da shugabanta Joseph Kony, ba shi ba.


Asalin hoton, Reuters

Mr Ongwen ya zama babban kwamandan LRA

Asalin hoton, AFP
Kungiyar LRA ta gallabi tsakiyar Afirka cikin shekara 20

'Yan kasar Uganda suna kallon yadda shari'ar ke gudana