Wani dan Tanzaniya na cigiyar macen aure

Tanzaniya
Bayanan hoto,

Mchambua ya ce bai kamata 'yan uwansa su samo masa mata ba, domin sune za su dinga kula da ita

Wani dan kasar Tanzaniya, Athumani Mchambua, ya bayyana aniyarsa ta neman aure domin maye gurbin matarsa wadda ta mutu.

Mchambua mai shekara 75, ya kafa allon cigiyar macen da za ta aure shi a unguwar Mbagala ta marasa galihu da ke Dar es Salaamn.

A cigiyar da ya rubuta a allon da harshen Swahili, ya bukaci duk mai son aurensa ta zama mai aiki tukuru wadda za ta iya aikin gona sannan ta kula masa da 'ya'yansa 11.

Bayanan hoto,

Mata hudu sun nuna sha'awarsu inda ya yi musu tambayoyi amma babu wadda ta cimma ka'idar da yake nema

Mista Mchambua ya shaida wa BBC cewar ya zabi ya nemi matar da zai aura da kansa ba sai 'yan uwa sun zabar masa ba kamar yadda al'ada suke yi a al'adance.

Ya kuma kara da cewar mata hudu sun nuna sha'awarsu inda ya yi musu tambayoyi amma babu wadda ta cimma ka'idar da yake nema, ya kuma ce wasu sun cika ka'ida biyu wasu kuwa daya suke da ita.

'Yar gidan Mchambua mai suna Dalia ta ce tana farin ciki da yadda mahaifinta ya tsara neman matar da zai aura, kuma a shirye take ta amince da duk wadda ta ci jarabawar mahaifinta.