Angela Merkel: Ya kamata a hana Musulmai sanya nikabi

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel

Asalin hoton, Getty Images

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta ce ya kamata a haramta sanya suturar nan mai rufe fuska watau Burka, ko nikabi a kasar idan zai yi wu ta fuskar doka.

Da take magana a taron jam'iyyarta, Misis Merkel ta ce bisa al'adar kasar, bai dace mata su rufe fuskarsu baki daya ba.

Wannan dai shiga ce da matan Musulmi ke yi, kuma an fi saninta da suna Burka a nahiyar Turai.

Idan aka bullo da tsarin dai, ba wai zai haramta sanya burka baki daya ba ne, a a, zai haramta wa mata sanya ta ne a wurare kamar makarantu da jami'o'i da kuma kotuna.

Kasashe da dama sun haramta sanya irin wannan tufafi a kasashen Turai.

Sai dai masu lura da al'amura na ganin shugabar na wannan magana ne domin samun karin goyon baya a zaben kasar da ke tafe.

Jam'iyyu masu adawa da baki na kara samun goyon baya a kasar, abin da ke tayar da hankalin Misis Merkel da jam'iyyarta.