Ana dab da murkushe Boko Haram - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce babu wata karamar hukuma a kasar dake hannun 'yan Boko Haram

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce babu wata karamar hukuma a kasar dake hannun 'yan Boko Haram

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya tabbatarwa kasashen duniya cewa ana dab da kawo karshen Boko Haram.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a wajen taron kasa da kasa kan tsaro da zaman lafiya a nahiyar Afrika da aka kammala a Dakar, babban birnin kasar Senegal.

Ya kuma yaba da irin gudummuwar tare da hadin kai da kasashe makwabata suke ba Nigeria wajen yaki da ta'addanci.

Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatarwa kasashen duniya cewa, al'amuran tsaro sun yi matukar inganta a Nigeria.

Ya ce "dakarun hadin guiwa na MNJTF sun shirya tsaf kuma sun amince a lokaci guda da aka amince tare da sauran dakarun soji su yi diran mikiya a maboyar Boko Haram don kawo karshen su ".

A cewar sa, yanzu sojojin kasar sun shiga dajin Sambisa kuma batun cewa akwai mayakan Boko Haram a yankin tafkin Chadi ya zama tarihi.

Shugaban Najeriyar ya ce jama'a musamman mazauna shiyyar arewa maso gabashin kasar sun tabbatar cewa babu wata karamar hukuma daga cikin kananan hukumomi 774 na kasar dake hannun 'yan Boko Haram.