Donald Trump ne ya fi kowa fice a duniya - in ji Mujallar Time

Shugaban kasar Amurka mai jiran gado Donald Trump

Asalin hoton, GERRY BROOME

Mujallar Time ta zabi Shugaban kasar Amurka mai jiran gado Donald Trump a matsayin mutumin da ya fi fice a duniya a 2016.

Hamshakin dan kasuwar ya samu kyautar ce bayan da ya doke Hillary Clinton a zaben Amurka, inda ya bai wa duniya mamaki.

Mista Trump ya shaida wa gidan talabijin na NBC bayan sanarwar cewa "ba karamar girmamawa ba ce" wacce ke da "matukar muhimmanci a wurinsa".

Misis Clinton da Shugaban Rasha Vladimir Putin na cikin wadanda Mista Trump ya doke wurin lashe kyautar.

Tsohon shugaban jam'iyyar UKIP ta Birtaniya, Nigel Farage, na cikin wadanda aka ware sunayensu saboda rawar da ya taka a zaben raba-gardamar da ya kai kasar ga ficewa daga Tarayyar Turai.

Misis Clinton ce ta zo ta biyu a zaben na Mujallar ta Time.