Bidiyo: Yadda zaben kasar Ghana ya kasance

Bayanan bidiyo,

Rahoton Ibrahim Isa kan yadda ake ci gaba da kasuwanci a mazabar Sawaba

Jama'a a Ghana sun fara kada kuri'a a zaben shugaban kasa inda masu sharhi ke cewa fafatawa za ta yi zafi tsakanin John Mahama da fitaccen jagoran adawa Nana Akufo Addo.

Shekaru 25 kenan da kasar Ghana ta koma turbar mulkin Dimukradiyya, kuma wannan shi ne karo na bakwai da al'umar kasar za su kada kuri'ar zaben shugaban kasa.

Akwai kuma wasu 'yan takarar da za su wakilci jam'iyyu hudu, da kuma daya mai zaman kansa.

Ga rahoton da Ibrahim Isa ya aiko mana da birnin Accra.