Pakistan: Mutum 47 sun mutu a hadrin jirgin sama

Jirgin sama

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A baya an zargi kamfanin jiragen kasar na PIA da rashin kula da lafiyar jiragensa

Wani jirgin sama mallakar kamfanin Pakistan International Airlines (PIA) dauke da fiye da mutum 40 ya fadi a Arewacin kasar.

Wata sanarwa da kamfanin ya fitar ta ce jirgin, mai lamba PK-661, "ya daina samun bayanai daga jami'an kula da jirage a kan hanyarsa ta zuwa Islamabad daga Chitral".

Wakiliyar BBC a kasar ta ce jirgin dan karami ne samfurin ATR.

Kafofin watsa labarai na Pakistan sun ambato 'yan sanda da kuma jami'ai na cewa jirgin ya fadi ne a kusa da garin Havelian, wanda bai da nisa da Arewacin Islamabad.

Hukumomi sun ce ana amfani da dukkan ma'aikata da kayan aiki domin gano inda jirgin ya ke.

A baya an zargi kamfanin jiragen kasar da rashin kula da lafiyar jiragensa, inda mutum 44 suka mutu a wani hadari a shekarar 2006.

Kungiyar Tarayyar Turai ta dakatar da jiragen kamfanin a 2007 saboda damuwa kan ingancinsu.