'Yan sanda sun kashe mutum 80 a Kenya

Ana binciken jami'an tsaro 300 bisa keta hakkin bil-adama a Kenya
Bayanan hoto,

Ana binciken jami'an tsaro 300 bisa keta hakkin bil-adama a Kenya

Kungiyar kare hakkin bil-adama ta Haki Africa da ke Kenya ta ce 'yan sanda sun kashe mutum fiye da 80 a yankin da ke kusa da gabar ruwa cikin shekara hudu da suka gabata.

Wata kungiyar kare hakkin bil-adama a kasar Kenya, mai suna Haki Africa, ta ce 'yan-sanda sun kashe mutane fiye da tamanin a cikin yanayi mai daure kai a yankin da ke kusa da gabar ruwa cikin shekaru hudu da suka gabata a yakin da

Hukumomi na zargin yawancin mutanan ne da kasancewa mambobin kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayin Islama.

Daraktan zartaswa na Kungiyar, Hussein Khalid, ya ce adadin ma ka iya fin haka, domin wasu iyalai na fargabar fitowa su bayyana abin da ya faru da 'yan uwansu.

Kungiyar ta ce wadanda lamarin ya rutsa da su, an kashe su ne lokacin dirar mikiya kan masu zanga-zanga da kuma wasu taruka a inda ake zargin ana cusawa matasa tsattsauran ra'ayi.

Wata hukumar sa ido kan 'yan sanda ta ce ana binciken jami'ai 300 bisa zargin keta hakkin bil'adama.