Ghana: 'Zan iya yin tsirara idan jam'iyyata ta lashe zabe'

Ba a kai kayan aiki da wuri ba a wasu mazabu
Bayanan hoto,

Yadda zaben Ghana ya gudana

Yayinda ake cigaba da kidaya kuri'ar babban zaben kasar Ghana da aka kaɗa ranar Laraba, magoya baya na ta tofa albarkacin bakinsu kan inda suke ganin nasara za ta kaya.

Kowa dai na ganin jam'iyyarsa ce za ta lashe zaben.

Wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai ya tattauna da wasu matasa bayan kammala kada kuri'unsu.

Kuma a cikin su har da wanda yake cewa idan dai har jam'iyyarsa ta lashe zaben to zai iya yin tubewa tik saboda murna.

Ku saurari hirar domin jiyewa kunnuwanku:

Bayanan sauti

Manyan 'yan takara a zaben Ghana

Ana dai sa ran fitar da sakamakon zaben na kasar Ghana ranar Asabar.

Sai dai kuma idan ba a samu dan takarar da ya sami kuri'un da suka haura kaso 50 cikin 100 na kuri'un da aka kada ba, to za a je zagaye na biyu na zaben.