Mata 100 : Dalilan mutuwar aure a kasar Hausa

Hafsat Abdulwaheed
Bayanan hoto,

Hajiya Hafsat Abdulwaheed ta rubuta littattafai fiye da 30

Yawan mutuwar aure na cikin manyan matsalolin da ke ci wa mata tuwo a kwarya a kasar Hausa.

Sau da yawa dai, matsalar kan jefa mata cikin mawuyacin hali, musamman idan an bar su da kananan yara.

Tana kuma cikin batutuwan da mata marubuta suka fi mayar da hankali a kansu a rubuce-rubucensu.

Hajiya Balaraba Ramat Yakubu da Hajiya Hafsat Abdulwaheed sun tattauna a kan wannan matsala, a wani banagre na rufe shirye-shiryen BBC na musamman na Mata 100: Muryar Rabin Al'ummar Duniya.

A tattaunawar tasu sun lissafa wadannan abubuwan da suka ce a ganinsu suke haddasa mutuwar aure:

  • Kwadayin dukiya daga mahaifan yarinya da ita yarinyar kanta
  • Karya daga bangaren maza
  • Rashin binciken asalin saurayi
  • Kazantar 'ya mace
  • Mugayen kawaye masu ba wa mace muguwar shawara
  • Rashin ladabi ga miji
  • Rashin hakuri daga bangaren maza