Saudiyya da Iran na amfani da kasashe wajen yakar juna

Burtaniya ce babbar kawar Saudiyya
Bayanan hoto,

Sakataren harkokin waje na Burtaniya, Boris Johnson

Sakataren Harkokin kasashen Waje na Burtaniya, Boris Johnson ya zargi Saudiyya wadda daya ce daga cikin manyan kawayen Burtaniyar, da yakin sari ka noke a gabas ta tsakiya.

Jaridar The Guardian ta wallafa wani bidiyo na mista Johnson a inda yake shaidawa wani taron manema labarai cewa Saudiyya da Iran suna yakar juna ta hanyar yin amfani da wasu kasashe.

Kasashen biyu dai sun yi kaurin suna wajen yakar bangarorin da ba sa yin su a Syria da Yemen.

Wani mai magana da yawun ma'aikatar ta kasashen waje ya ce mista Johnson ya bayyana karara cewa Saudiyya babbar kawar Burtaniya ce.

Ya kuma kara da cewa Burtaniyar na taimaka wa Saudiyyar wajen kare iyakokin da burin manufofin al'ummarta.