Ghana: An yi kutse a shafin intanet na hukumar zabe

An electoral official overturns a ballot box prior to counting votes at a polling station in Tamale, northern region, on December 7, 2016.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Fiye da mutum miliyan 15 ne suka yi rijista domin kada kuri'a

Masu satar bayanai sun yi kutse a shafin intanet na hukumar zabe ta kasar Ghana a daidai lokacin da ake kirga kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasa da 'yan majalisa.

Hukumar ta ce shafin ya dawo aiki, amma kawo yanzu ba a san ko su waye suka aikata hakan ba.

Ta kuma aika sakon Twitter da ke neman jama'a da su yi watsi da "sakamakon boge" da ake wallafa wa a shafukan sada zumunta.

Masu sharhi dai na ganin cewa fafatawar za ta yi zafi ne tsakanin John Mahama da fitaccen jagoran adawa Nana Akufo Addo.

Duka 'yan takara bakwai na zaben sun yi alkawarin tabbatar da zaman lafiya.

Batun tabarbarewar tattalin arziki da kuma cin hanci da rashawa su ne suka mamaye yakin neman zaben.

Zaben na ranar Laraba ya tafi lami-lafiya, sai dai an dage kada kuri'a a wata mazaba zuwa ranar Alhamis bayan an kai kayan zabe a makare.

Za a gudanar da zagaye na biyu nan gaba a wannan watan idan babu wanda ya samu fiye da kashi 50% a cikin manyan 'yan takarar biyu.

Shugaba Mahama ya kayar da Mista Akufo-Addo da kuri'u kasa da 300,000 a zaben 2012.

Nan da kwanaki biyu ake sa-ran samun cikakken sakamakon zaben.

Asalin hoton, Twitter

Bayanan hoto,

Jama'a sun fara yada sakamakon boge a shafukan intanet

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Masu sharhi na ganin fafatwa za ta yi zafi tsakanin John Mahama da fitaccen jagoran adawa Nana Akufo Addo

Bayanan hoto,

Tun cikin dare wasu mutanen suka kama layi ta hanyar ajiye duwatsu

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ana sa ran samun sakamakon zaben cikin kwanaki uku