Fargaba kan jinkirin sakamakon zabe a Ghana

  • Yusuf Ibrahim Yakasai
  • BBC Hausa, Kumasi, Ghana
Takardun zabe a Ghana

Majalisar tabbatar da zaman lafiya ta Ghana ta yi kira ga hukumar zaben kasar EC da ta gaggauta sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a ranar Laraba.

Shugaban Majalisar Farfesa Emmanual Asante ne ya yi kiran a wajen wani taron manema labarai.

Farfesa Asante ya ce jinkiri wajen bayyana sakamakon ya na haifar da fargaba, da rashin tabbas, da kuma yada jita-jita mara amfani.

Ya kuma yi kira ga jam'iyyun siyasa da jama'ar kasar su kwantar da hankula, su kuma jira hukumar zaben kasar ta bayyana sakamako.

A nata bangaren, hokum zaben kasar ta ce jinkirin na da nasaba da matsalolin da aka samu a wurin yin zaben fiye da kima.

Hukumar ta ce don haka sai ta sake tantanace duka sakamakon da aka kawo mata, kafin ta kai ga bayyana wa.

Ita kuwa gamayyar kungiyoyin fararen ta cikin gida da ta saka ido kan zaben, CODEO, ta ce zaben yana da inganci.

CODEO ta kuma yi Allah-wadai da yadda jam'iyyun siyasa ke bayyana sakamakon zabe, gabanin hukumar zabe.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Fiye da mutum miliyan 15 ne suka yi rijista domin kada kuri'a

A wani labarin, bayanai sun ce jakadan Amurka a Ghana ya kai ziyara ga dan takarar jam'iyyar hamayya Nana Akuffo Ado a gidansa da safiyar ranar Alhamis.

Gidan talabijin na Joy News mai zaman kansa ya rawaito cewa mutanen biyu sun gana a asirce, kuma babu wanda ya san abin da suka tattauna.