BBC na kara sunayen muhimman mata a Wikipedia

Shirin mata 100 na BBC

Ma'aikatan BBC a Abuja sun bi sahun takwarorinsu na sassan duniya wurin wallafa karin sunayen mata wadanda suka taka muhimmiyar rawar gani a shafin intanet na Wikipedia.

WikiProject wani bangare ne na shirin BBC na mata 100 rabin muryar al'umma da ke fito da irin rawar da mata suka taka a duniya.

Baya ga ma'aikatan BBC, mun kuma gayyato wasu daga waje domin shiga cikin shirin.

Wasu daga cikin matan da aka sanya sun hada da:

Amina Mohammed: Ita ce ministar muhalli ta Najeria wacce aka nada a ranar 11 ga watan Nuwambar shekarar bara.

Amina ta taka muhimmiyar rawa wajen ayyana matakan cigaban al'umma lokacin tana mai bada shawara ta musamman ga Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon a kan matakan cigaban al'umma a 2015.

Bayanan hoto,

Aloma Mariam Mukhtar ita ce babbar joji mace ta farko a Najeriya

Aloma Mariam Mukhtar: Na daya daga cikin matan da za mu saka bayananta a shafin na Wikipedia. An haife ta ne a ranar 20 ga watan Nuwambar shekarar 1944.

Aloma ta zamo mace ta farko a fagen rayuwa da dama a Najeriya.

Ita ce mace lauya ta farko a arewacin Najeriya kuma mai shari'a mace ta farko a babbar kotun jiha da ke Kano a arewacin kasar.

Baya ga haka ita ce mace mai shari'a ta farko a kotun daukaka kara ta Najeriya.

Aloma ta kuma kasance mace ta farko mai shari'a a kotun kolin Najeriya sannan kuma mace ta farko da ta yi aikin a matsayin babbar jojin Najeriya.

Bayanan hoto,

Baya ga ma'aikatan BBC, mun kuma gayyato wasu daga waje domin shiga cikin shirin

Hafsat Abdulwaheed: Na daya daga cikin matan da suka taka muhimmiyar rawar gani a Najeriya amma kuma babu bayananta a shafin wikipedia.

A don haka tana daya daga cikin matan da za mu wallafa bayannanta a shafin.

Hafsat Abdulwaheed tana rubutun zube da wakoki kuma ita ce mace ta farko da aka wallafa littafinta na kagagen labari a harshen Hausa.

Hafsat ta taba yunkurin tsayawa takarar gwamna a jihar Zamfara a shekarun 2000.

Za ku iya kasancewa tare da mu kai tsaye a shafinmu na Facebook daga karfe 11 na safe a ranar Alhamis domin ganin yadda za mu tafiyar da aikin WikiProject inda za mu kara bayannan wadannan matan da wasu daban wadanda suka cancanta a kara bayanansu.