Ko waye zai lashe zaben kasar Ghana?

Bayanan bidiyo,

An girke jami'an tsaro a kofar Hukumar zaben Ghana

Al'ummar kasar Ghana na cigaba da dakon sakamakon zaben shugaban kasa da 'yan majalisar da suka kada, yayin da rahotanni ke nuna cewa 'yan adawa sun taka rawar gani.

Shugabar Hukumar Zaben Charlotte Osei ta ce sun samu sakamakon mazabu 210 a cikin 275, amma wasu wakilan jam'iyyu sun ki sanya hannu a kan wasu sakamakon.

Nan gaba a ranar Juma'a ake sa ran hukumar za ta fara bayyana sakamakon, kuma mai yiwuwa a bayyana wanda ya yi nasara.

Sai dai kafafen yada labarai na kasar sun ce sakamakon da suka samu ya nuna cewa jagoran adawa Nana Akufo Addo ne akan gaba.

Amma Shugaba John Mahama ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa "ya kamata a bai wa hukumar zaben damar yin ayyukanta kamar yadda tsarin mulki ya tanada... duk yadda sakamakon zai kasance".

Jinkiri wurin bayyana sakamakon na cigaba da haifar da fargaba a tsakanin 'yan kasar.

Madam Charlotte Osei ta kuma nuna takaici kan adadin mutanen da suka fito domin kada kuri'a.

A ranar Alhamis Majalisar tabbatar da zaman lafiya ta Ghana ta yi kira ga hukumar zaben kasar zaben da ta gaggauta sanar da sakamakon zaben da aka yi a ranar Laraba.

Shugaban Majalisar Farfesa Emmanual Asante ya ce jinkiri wajen bayyana sakamakon ya na haifar da fargaba, da rashin tabbas, da kuma yada jita-jita mara amfani.

Ya kuma yi kira ga jam'iyyun siyasa da jama'ar kasar su kwantar da hankula, su kuma jira hukumar zaben kasar ta bayyana sakamako.

Jami'an tsaro na sunturi a wurare da dama a kasar domin kaucewa tashin hankali.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wakilan jam'iyyu na ci gaba da tattara sakamakon zaben

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An girke jami'an tsaro a wurare da dama a kasar domin kaucewa tashin hankali

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Fiye da mutum miliyan 15 ne suka yi rijista domin kada kuri'a