'Yadda mijina ya so ya kashe ni saboda ba na haihuwa'

  • UmmulKhairi Ibrahim
  • BBC Hausa, Abuja
Bayanan bidiyo,

Mijin Victoria ya nemi ya kashe ta duk da irin soyayyar da suka yi a baya

Victoria John, wata mazauniyar kauyen Lakwushehe ce da ke Jos, a jihar Plateau a Najeriya.

Victoria ta kasance daya daga cikin matan da suka fuskanci musgunawa da kyama sakamakon rashin haihuwa.

Wannan baiwar Allah dai ta hadu da mijin da ta aura, a jami'a, a inda kuma suka yi soyayya sannan daga bisani suka yi aure.

To amma kash! Farin cikin Victoria ya fara gushewa ne tun lokacin da ita da angonta suka je wurin likita kan batun haihuwa.

Bayanan hoto,

Victoria tana nuni da hotonta lokacin da aka yi mata aure tare da angonta

Mijin nata ya fara dandana mata kudarta bayan da likitan ya sanar da su cewa Victoria ba za ta iya haihuwa ba.

Lokacin da Maman Philip wadda ita ce mahaifiyar Victoria, ta ga 'yarta ta dawo gida, hankalinta ya tashi fiye da aniya.

Na yi kokari na ji ta bakin mijin Victoria amma kuma abin ya ci tira.

Ga dai abin da Victoria ta shaida min a hirar da na yi da ita:

Bayanan sauti

Lokacin da Maman Philip ta samu labarin abin da ya dawo 'yarta gida ba ta ji dadi ba

Wasu alkaluma da hukumar lafiya ta duniya ta fitar a 2004 sun nuna cewa fiye da kaso 30 cikin 100 na mata masu shekaru 25 zuwa 49, na fama da wannan matsala.

Hukumar ta kara da cewa matan masu irin wannan matsalar sun fi yawa a yankin Afirka da ke kudu da Sahara.

A Najeriya kuwa kashi 10 cikin 100 na ma'aurata ne ke fama da irin wannan matsala da Victoria John ta fuskanta.

Bayanan hoto,

Victoria ta ce ba ta fatan matsalar rashin haihuwa ta sami ko da abokin gabarta