Birtaniya na leken asirin shugabannin Afirka

Ya kuma ce daga bisani Burtaniyar ta ba wa Amurka takardun
Bayanan hoto,

Edward Snowden ne ya fallasa asirin

Wata jaridar Faransa mai suna Le Monde, ta ce tana dauke da wasu takardun shaida da ke nuni da cewa Ma'aikatan Leken Asirin Birtaniya sun leko asirin shugabanni da kungiyoyin tawaye na kasashe 20 a Afirka.

Jaridar ta ce ta samu bayanan ne da aka tara daga 2009 zuwa 2010 ta hannun dan Amurkar nan mai fallasa wanda ke gudun hijra a Russia, wato Edward Snowden.

Jaridar ta kara da cewa jami'an leken asirin na Burtaniyar sun jefa komarsu ne a kan mutane da suka hada da shugaban Kenya Mwai Kibaki da na Angola, Eduardo Santos.

Har wa yau, jaridar ta ce Burtaniya ta kuma mika wa Amurka takardun daga bisani.