Majalisar Korea ta kudu ta tsige Park Geun-hye

Park Geun-hye

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Tun cikin shekarun 1970 Ms Park da Ms Choi suke kawancensu

Majalisar Korea ta kudu ta kada kuri'ar tsige shugaba Park Geun-hye a kan badakalar cin hanci.

An amince da kudirin da kuri'a 234 yayinda da 56 suka kada kuri'ar kin amincewa; hakan kuma na nufin cewa wasu mambobin jam'iyyar Saenuri na Ms Park sun amince da kudirin.

A halin yanzu Hwank Kyo-ahn, firai ministan kasar ne ya ke rikon kwarya.

Dubban mutane ne suka bazama a tituna a makonnin da suka gabata inda suka bukaci a tsige Ms Park. Bayan an kada kuri'a , sai ta kara bayar da hakuri inda ta:

"Rashin kulawar ta ce ta haddasa hargitsin da ake fuskanta a kasar".

Dangantakar da ke tsakanin Choi Soon-sil da Ms Park ce ta haddasa rikicin, inda ake zarginta da yin amfani da irin damar da take da shi wajen samun kudi da yin tasiri.

Choi tana hannun jami'an tsaro inda ake tuhumarta da tursasawa wani ya aikata abu da kuma yin amfani da matsayinta ta hanyar da bata dace ba.

Masu shigar da kara sun ce Ms Park ta taka rawa a zargin cin hancin da ake yi, zargin da ta musanta.