Zaben Ghana: Jagoran 'yan adawa Akufo-Addo ya samu nasara

Nana Akufo-Addo

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Sau uku Nana Akufo-Addo yana tsayawa takara

Hukumar zaben kasar ta bayyana jagoran 'yan adawa Nana Akufo-Addo a matsayin wanda ya lashe zaben kasasr shugaban kasar na ranar Laraba.

Shugabar Hukumar Charlotte Osei ta ce Mista Akufo-Addo ya samu kashi 53.85 cikin dari, yayin da shugaba mai ci John Mahama ya samu kashi 44.40.

Tun da farko shugaban ya amince da shan kaye a hannun Mista Akufo-Addo, inda ya taya shi murna.

Mista Akufo-Addo ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa shugaba Mahama ya kira shi ta waya inda ya taya shi murnar lashe zaben.

Wakilin BBC a birnin Accra ya ce jama'a suna ta murnar wannan sanarwar da aka bayar.

Wannan ne karo na farko da shugaba mai ci ya sha kaye a zaben Ghana tun bayan da kasar ta fara amfani da tsarin jam'iyyu maus yawa a 1992.

Kashi 68 cikin dari na wadanda suka yi rijista ne dai suka kada kuri'a.

Bayanan bidiyo,

An girke jami'an tsaro a kofar Hukumar zaben Ghana

Nasarar ta zo wa Mista Addo, wanda lauya ne mai shekara 72, a karo na uku, domin sau biyu yana shan kaye a baya.

An dade ba a bayyana sakamakon zaben ba, abin da ya kawo zaman zullumi a kasar.

Hakan ne kuma ya sa aka girke jami'an tsaro a sassan kasar da dama, yayin da 'yan siyasa da malamai suka yi kiran da a zauna lafiya.

Ya yi alkawarin kafa masana'anta a dukkan mazabu 216 da ke kasar.