Zaben Gambia: Me ya sa Yahya Jammeh ya yi amai ya lashe

Adama Barrow (L) Yahya Jammeh

Asalin hoton, Reuters/AFP

Bayanan hoto,

Shugaba mai jiran gado Adama Barrow (daga hagu) ya yi Allah-wadai da kalaman Yahya Jammeh

Shugaban Gambia mai barin gado, Yahya Jammeh ya yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasar wanda da farko ya amince da shan kaye.

Yahya Jammeh ya sha kaye daga abokin takararsa, Adama Barrow, bayan da ya samu kaso 43 na kuri'ar da aka kada.

A makon da ya gabata ne dai Yahya ya amince da shan kaye, a inda ya kira abokin takarar tasa domin taya shi murna.

Mista Jammeh ya ce ya janye matsayinsa na farko ne bayan la'akari da cewa ba a kidaya kuri'un daidai ba.

Ya kuma kara da cewa shi ne mutumin da ya lashe zaben da fifikon kuri'a 87,000.

Sai dai kungiyar Tarayyar Afirka ta yi Allah-wadai da kalaman na sa, tana mai cewa "bakin alkalami ya riga ya bushe".

Wata sanarwa da Shugabar kungiyar Dlamini-Zuma ta fitar, ta yi kira ga Shugaba Jammeh da ya tabbatar ya bayar da hadin kai wurin mika mulki ga sabuwar gwamnati cikin lumana.

Ita ma Amurka ta nuna takaicinta kan yadda shugaban mai barin gado ya bsauya matsaya kan sakamakon zaben.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yahya Jameh ya hau mulki ne ta hanyar juyin mulki

A 1994 dai Yahya Jameh ya hau mulkin kasar, bayan juyin mulkin da ya jagoranta a kasar.

Mista Barrow ya zargi shugaban mai ci da kokarin lalata tsarin demokuradiyya ta hanyar yin kin amincewa da sakamakon zaben.

Sai dai jami'ansa sun ce shugaba mai jiran gadon yana nan cikin koshin lafiya.

Hukumar zaben kasar ta sake duba sakamakon zaben a ranar 5 ga watan Disamba bayan da aka gano cewa an yi kuskure a wata mazaba, abin da ya kara wa Mista Barrow yawan kuri'u.

Kuskuren ya haifar da kara kuri'u ga wasu 'yan takarar ma, sai dai bai sauya yadda sakamakon ya kasance ba, a cewar hukumar.

Sai dai ya rage adadin tazarar da Mista Barrow ya bayar daga kashi 9 cikin dari zuwa kashi 4.