Rasha ta 'tallafa wa Donald Trump' wurin samun nasara

Donald Trump da Hillary Clinton

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Donald Trump ya kayar da Hillary Clinton ne a zaben na watan Nuwamba

Jami'an leken asirin Amurka sun yi amannar cewa Rasha ta yi kokarin tallafa wa Donald Trump domin ya samu nasara a zaben kasar.

Wani rahoto da jaridar New York Times ta wallafa ya ce jami'an na da kwarin giwa cewa Rasha ta yi kutse a na'urorin kwamfiyutar kasar.

Wani bincike da hukumar CIA ta yi wanda jaridar Washington Post ta buga ma ya tabbatar da irin wannan ikirari.

Sai dai Mista Trump ya yi watsi da kalaman na CIA, yana mai cewa: "Wadannan su ne fa mutanen da suka ce Saddam Hussein ya mallaki makaman kare-dangi."

Jami'an Rasha dai sun sha musanta wannan zargi.

A ranar Juma'a ne Shugaba Barack Obama ya umarci ma'aikatar leken asirin kasar da ta sake duba batun kutsen bayanai a lokacin zaben.

Mai magana da yawun fadar White House ya bayyana binciken da wani al'amarin da zai yi nutso cikin badakalar kutse tun daga shekarar 2008.

Wasu na ganin wannan mataki dai kamar wata bita-da-kulli ce gwamnatin Democrat bai barin gado ke yi wa Mista Trump kan nasarar da ya samu.