Ronke Adeniroye manomiya ce 'yar Nigeria

Ronke Adeniroye tana kokarin kawo sauyi a tattalin arzikin Nigeria ta hanyar noma, inda take fafutukar wayar da kan matasa kan su rungumi sana'ar.

Haka kuma tana kokarin kawo karshen kwararar matasa daga kauye zuwa birni, inda suke barin gonaki ba a nomansu, sannan su dawo birni suna zaman kashe wando.