Tashin bama-bamai a kusa da filin wasa na Istanbul

Yadda hayaki ya turnuke wurin kenan a ranar 10 ga Disambar 2016

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An so kai harin ne kan 'yan sandan kwantar da tarzoma

Rahotanni daga kasar Turkiyya na cewa akalla 'yan sanda 29 ne suka mutu sannan karin mutane fiye da 70 sun jikkata sakamakon tashin wasu bama-bamai guda biyu a kusa da filin wasa na birnin Instanbul.

Hukumomin Turkiyya sun ce 'yan kunar bakin-wake ne suka kai hare-haren a motoci da nufin kashe wasu 'yan sanda.

Wadanda suka shaida yadda al'amarin ya faru sun ce sun ji karar harbin bindiga bayan bama-baman sun tashi awa biyu bayan tashin 'yan wasa.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari.

Sai dai kuma kungiyar mayakan sa-kai na Kurdawa da kungiyar IS sun sha ikrarin kai hare-hare irin wannan.

Hare-haren da aka kai Turkiyya a wannan shekarar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wurin da aka kai harin bam a Ankara ranar 13 ga Maris

20 Agusta: Harin bam din da ya kashe mutane 30 a wani wurin bikin aure a Gaziantep

30 Yuli: An kashe mayakan Kurdawa 35 wadanda suka yi yunkurin kai hari kan sansanin sojojin Turkiyya

29 Yuni: Harin bam da bindigar da ya kashe mutum 41 a filin jirgin sama na Attaturk da ke Istanbul

13 Maris: Mutane 37 sun mutu a wani harin kunar-bakin-wake da mayakan Kurdawa suka kai Ankara

17 Fabrairu: Lokacin da mutum 28 suka mutu a wani harin da aka kai kan jerin gwanon motocin sojoji a Ankara

Bayanan hoto,

Hotunan yadda wasu 'yan sanda suke kokarin taimakon abokan aikinsu da suka jikkata ranar 10 ga Disamban 2016