Za'a cafke dan kwangilar cocin da ya rufta a Nigeria

Bayanan bidiyo,

Babu murya a wannan bidiyon

Hukumomi a Nigeria sun bada umarnin cafke dan kwangilar da ke aiki a cocin da ya rufta a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom inda gwamman mutane suka rasa rayukansu.

Sai dai hukumomi sun nace cewa mutum 27 ne suka mutu, yayin da rahotanni ke cewa adadin wadanda suka mutun ya kai 100.

Rahotanni sun ce ginin na majami'ar Reigners Bible Church ya rufta ne a lokacin da ake bikin nada shugabanta a matsayin Bishop.

Tuni hukumomi suka bayar da umarnin kama dan kwangilar da yake aikin ginin cocin.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aike da jaje tare da ta'aziyya ga al'ummar jihar.

Gwamnan jihar Udom Emmanuel na cikin wadanda suka tsallake rijiya da baya, kuma Shugaba Buhari ya taya shi murna kan kubutar da ya yi.

Mista Emmanuel ya ce za a gudanar da bincike kan lamarin inda ya bada umurni a cafke dan kwangilar da ke aikin gina cocin.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Garba Shehu ya fitar, Shugaba Buhari ya nemi al'umma da su agazawa mutanen da suka jikkata a hadarin.

Kafafen yada labarai a Najeriya sun ambato wadanda suka shaida lamarin na cewa ana kan yi wa ginin kwaskwarima saboda hasashen cewa jama'a da dama za su halacci taron.

Asalin hoton, Daily Post

Bayanan hoto,

Ana cigaba da aikin ceton wadanda lamarin ya ritsa da su

Wani ganau ya ce "Ana cikin bikin nada Fasto Akan Week kwatsam sai ginin ya rufta baki daya".

Ya kara da cewa "Mutane da dama sun makale a kuraguzan ginin a daidai lokacin da masu aikin ceto ke cigaba da kai dauki."

Shafin labarai na Premium Times ya ce an garzaya da wadanda suka ji raunuka zuwa asibitoci da dama a fadin birnin.

Ana yawan samun ruftawar gine-gine a Najeriya, abin da masu sharhi ke alakanta wa da rashin bin doka da amfani da kayan aiki marasa kyau.

Akalla mutum 115 ne suka mutu a watan Satumbar 2014 lokacin da wani gini mallakar Cocin Fasto TB Joshua ya rufta a birnin Lagos.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Jama'a na jimamin abin da ya faru

Bayanan hoto,

Birnin Uyo na Kudu maso Kudancin Najeriya ne