Nigeria: Bidiyon ruftawar ginin coci a Akwa Ibom

Akalla mutum 60 ne suka mutu bayan da wani ginin coci ya rufta a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom a kudancin Najeriya.

Rahotanni sun ce ma'aikata na kokarin kammala ginin cocin ne kafin bikin nada wani bishop.