Wa Donald Trump zai nada sakataren harkokin waje?

Rex Tillerson

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Rex Tillerson ya kasance shugaban Exxon Mobil tun 2006

Shugaban katafaren kamfanin mai na Exxon Mobil Rex Tillerson ya gana da Shugaban Amurka mai jiran gado a daidai lokacin da yake ci gaba da neman wanda zai nada sakataren harkokin waje.

Gidan talabijin na NBC ya ambato wasu makusantan Donald Trump na cewa akwai yiwuwar a bayyana sunan Mista Tillerson a mako mai zuwa.

Za kuma a nada tsohon jakadan kasar a Majalisar Dinkin Duniya John Bolton a matsayin mataimakinsa.

Wannan labari na zuwa ne a daidai lokacin da Mista Trump da tawagarsa suka yi watsi da ikirarin jami'an leken asirin kasar cewa Rasha ta yi kutse domin taimaka masa yin nasara a zabe.

Fitaccen dan Jam'iyyar Republican Mitt Romney na cikin wadanda ake dangantawa da mukamin.

A makon da ya gabata ne tsohon Magajin Garin birnin New York Rudy Giuliani ya janye da bukatar neman mukamin.

Harkokin kasuwancin Mista Giuliani sun sa ana nuna shakku kan dacewarsa.

Mista Tillerson, mai shekara 64, yana da kwarewa sosai a harkokin kasuwanci na duniya da kuma huldar kasuwanci da Shugaban Rasha Vladimir Putin.

Ya kuma soki takunkumin da kasashen duniya suka sanya wa kasar bayan da ta mamaye yankin Crimea.