Za a saka wa Jammeh takunkumi idan ya ci gaba da zama a kan mulkin Gambiya

Zaben Gambia

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Ana ta saka wa Jammeh matsi kan ya sauka daga kan karagar mulki

Shugaban tawagar majalisar dinkin duniya da ta kai ziyara Gambiya, Mohammed Ibn Chambers, ya ce za a saka wa Yahya Jammeh takunkumi mai tsauri, idan har ya ce zai ci gaba da zama a kan karagar mulkin kasar.

Ibn Chambers ya kuma yi kira ga sojojin gwamnatin Gambiya da su bar ofishin hukumar zaben kasar da suka mamaye tun a ranar Talata.

Chambers ya ce "hakan da suka yi tamkar rashin mutunta amincewar al'ummar Gambiya ne".

Tun farko Jammeh wanda ya shugabanci Gambiya shekara 22, ya amince da sakamakon zaben kasar da aka gudanar wanda Adama Barrow ya yi nasara, daga baya ya sauya ra'ayinsa.

Daga nan ne kuma ya kalubalancin sakamakon zaben a babbar kotun Gambiyar.

Ibn Chambers wanda ya ziyarci Gambiya a ranar Talata ya ce, shigar da kara da Jammeh ya yi ya sha bam-bam da kayen da ya sha.

Ya kara da cewar ya kamata Jammeh ya sauka daga kan mulkin da wa'adinsa zai kare a ranar 16 ga watan Janairu.