Aikin dan sanda a Burtaniya sai mai digiri daga shekarar 2020

Aikin 'yan sandan Burtaniya sai mai digiri
Bayanan hoto,

Ana samun karuwar aikata miyagun laifuka ta intanet

Kwalejin aikin dan sanda ta Burtaniya ta ce daga shekarar 2020 ba za ta dauki masu sha'awar yin aiki ba sai wadanda suka mallaki shaidar karatun digiri.

Kwalejin ta ce ta haka ne za ta samar da sauyin da ake bukata domin yakar masu aikata laifuffuka.

Babban jami'in 'yan sandan Burtaniya ya ce sauyin ma'aikata da za a samar zai taimaka wajen inganta aikin ta yadda za su dunga sa ido da aikin sintiri ta kafar intanet.

Shugaban kwalejin, Alex Marshall, ya ce yanzu aikin jami'an tsaro ya sauya matuka.

Ya kuma ce "Aikata miyagun laifuka na karuwa ta intanet, saboda haka akwai bukatar ma'aikata masu ilimin zamani wadanda za su iya tattara bayanai su kuma nemo mafita".