Donald Trump ya nada Tillerson sakataren harkokin waje

Rex Tillerson

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Rex Tillerson ya kasance shugaban Exxon Mobil tun 2006

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya zabi Shugaban katafaren kamfanin mai na Exxon Mobil Rex Tillerson domin ya kasance sakataren harkokin waje a gwamnatinsa.

A wata sanarwa da ya fitar, Mista Trump ya ce Mista Tillerson na daya daga cikin "kwararrun 'yan kasuwa da suka kware wurin kulla alaka" a duniya.

Mista Tillerson, mai shekara 64, yana da alaka mai kyau da Shugaban Rasha Vladimir Putin, abin da ke damun wasu 'yan jam'iyyar Republican ta Mista Trump.

Ya kuma soki takunkumin da kasashen duniya suka sanya wa kasar bayan da ta mamaye yankin Crimea.

Yana bukatar amincewar majalisar dattawa kafin nadin na sa ya tabbata.

Wannan labari na zuwa ne a daidai lokacin da Mista Trump da tawagarsa suka yi watsi da ikirarin jami'an leken asirin kasar cewa Rasha ta yi kutse domin taimaka masa yin nasara a zabe.

Fitaccen dan Jam'iyyar Republican Mitt Romney na cikin wadanda aka yi hasashen za su samu mukamin.

A makon da ya gabata ne kuma tsohon Magajin Garin birnin New York Rudy Giuliani ya janye da bukatar neman kujerar.

Harkokin kasuwancin Mista Giuliani sun sa ana nuna shakku kan dacewarsa.