BBC na neman sabbin ma'aikata

Ma'aikatan BBC Abuja
Bayanan hoto,

BBC na da ma'aikata daga sassan duniya da daban-daban

Wata babbar dama ta samu ga BBC... da ku ma.... Kafar watsa labarai ta BBC na bunkasa kuma muna so mu tafi tare da ku!

Shin kuna bukatar nuna bajintar da Allah ya hore maku, sannan miliyoyin mutane su ga irin kwarewarku da aikinku a kullum? To babu shakka muna da aikin da ya dace da ku.

BBC na neman babban dan jarida wanda ya goge a fannin hulda da shafukan sada zumunta.

Muna neman mutumin da ke da basira da hangen nesa da kuma sha'awar aikin yada labarai.

Ya kamata ka kasance mai sha'awar kafafen sadarwa na zamani da kuma fahimtar irin rawar da BBC ke takawa a fadin duniya. Kai za ka jagoranci al'amuran yau da kullum na shafukan sada zumunta na Sashen Hausa na BBC.

Kana bukatar kwarewa da gogewa a fannin aiki a fagen watsa labarai ta hanyoyin sadarwa na zamani da kuma sha'awar mu'amala da shafukan sada zumunta da fahimtar irin cigaban da ake samu a fannin da ma sauran fannoni masu alaka da shi.

Ya kamata ka zama mai idon zakulo ingantattun labarai da bayar da su ta hanyoyin sadarwa na zamani a cikin harshen Hausa da Ingilishi, da kuma iya amfani da manhajar harhada bidiyo.

Bayanan hoto,

Duka wadannan guraban ayyuka za su kasance ne a ofishin BBC da ke Abuja

Nemi aikin babban dan jarida wanda ya goge a fannin hulda da shafukan sada zumunta na BBC Hausa ta hanyar latsa wannan rariyar.

Za a rufe shafin a ranar 28 ga watan Disamba na 2016

Ga wata karin damar

Sashin Hausa na BBC neman mai shirya labaran bidiyo na zamani

Kafar watsa labarai ta BBC na bunkasa kuma muna so mu tafi tare da kai!

Muna neman Hausawa wadanda suke da hangen nesa da kuma matukar sha'awar aikin jarida.

Mutanen da suke son bayar da labari sannan suka fahimci irin rawar da BBC ke takawa a fadin duniya.

Nemi aikin mai shirya labaran bidiyo na sashin Hausa na BBC a Abuja. Domin samun wannan dama latsa wannan rariyar.

Za a rufe shafin ne daga ranar 28 ga watan Disamba