Rikicin Yemen: Amurka ta dakatar da sayar wa Saudiyya makamai

A watan Maris na 2015 Saudi Arabia ta soma mara wa Shugaba Hadi baya domin kawar da 'yan tawaye

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A watan Maris na 2015 Saudi Arabia ta soma mara wa Shugaba Hadi baya domin kawar da 'yan tawaye

Gwamnatin Amurka ta ce za ta rage yawan makaman da take sayar wa gwamnatin Saudiyya saboda fargabar da take yi cewa tana amfani da su domin kai wa farar-hular Yemen hare-hare ta sama.

Wani jami'i a ma'aikatar tsaron Amurka ta ce an daina sayar wa Saudiyya makamai masu linzami.

Gwamnatin Barack Obama ta ce tana fargabar cewa akwai "kura-kurai" kan hare-haren da Saudiyya ke kai wa a Yemen.

A watan Oktoba, jiragen yakin kawancen kasashen da Saudiyya ke jagoranta ya kashe sama da mutum 140 a kasar ta Yemen lokacin da suke zaman makoki.

Kawancen yana goyon bayan gwamnatin kasar ce a yunkurin da take yi na murkushe 'yan tawayen Houthi da ke samun goyon bayan Iran.