Dusar ƙanƙara ta kashe wani yaro a Amurka

Joshua Demarest

Asalin hoton, Family handout

Bayanan hoto,

Joshua Demarest dan wasan kwallon kafa ne

Wani yaro da ke yin wasa da wani curin dusar ƙanƙara bayan dusar ta rufe shi.

Joshua Demarest, mai shekara 13, ya mutu ne ranar Talata amma an gano abokinsa Tyler Day da ransa bayan shi ma curin dusar ƙanƙara ya rufe shi tsawon sa'o'i da dama a birnin na New York.

Ana tunanin cewa watakila motar da ke kwashe dusar ce ta sa ta rufe yaran saboda ta jibge ta a kan wani tsaunin dusar ƙanƙarar wanda ya yi rimi, kuma 'yan sanda sun ce Tyler ya gaya musu cewa ya yi karar motar kwashe dusar ƙanƙarar kafin lamarin ya auku.

An shafe sa'o'i da dama ana kwashe tan bakwai na dusar ƙanƙara daga garin Greenwich da ke New York.

'Yar uwar Tyler ce ta fara kiran masu bincike bayan da suka ga bai koma gida ba da misalin karfe biyar na yamma.

'Yan sanda, tare da taimakon karnuka ne suka bi hanyar da yaron ya bi inda suka gano shi a binne cikin dusar ƙanƙarar.

Asalin hoton, ABC

Bayanan hoto,

Tarin dusar ƙanƙara