An soma kwashe farar-hula daga Aleppo

An ce har yanzu akwai kimanin mutum 50,000 a gabashin Aleppo

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An ce har yanzu akwai kimanin mutum 50,000 a gabashin Aleppo

Jami'an kungiyar bayar da agaji ta Red Cross sun ce an soma kwashe farar-hula daga yankunan da ke hannun 'yan tawaye na birnin Aleppo da ke Syria.

Kungiyar bayar da agaji ta ICRC na fitar da mutum 200 da aka raunata daga birnin.

An ga jerin motocin daukar marasa lafiya da bas-bas na nufar gabashin birnin da zummar kwashe mutanen.

An yi tsammanin za ta kwashe mayaka da farar-hula daga birnin ranar Laraba, sai dai yajejejeniyar tsagaita wutar da aka kulla ta rushe.

Dakarun gwamnati sun kwace kusan dukkan yankunan da ke hannun 'yan tawaye a birnin na Aleppo a wannan makon bayan an kwashe shekara hudu ana gwabzawa.

Gidan talabijin din Syria ya ce za a kwashe 'yan tawaye da iyalansa 4,000 daga gabashin Aleppo zuwa ranar Alhamis.